Rahotanni na nuna alamomin soma samun rabuwar kawuna tsakanin ‘ya’yan APC kan mutumin da shugaba Buhari ke son zaɓa domin ya gaje shi a inuwar jam’iyyar.
A jiya Laraba mataimakin shugaban jam’iyyar APC reshan Arewa maso Yamma, Mallam Salihu Lukman ya aike da wata buɗaɗɗiyar wasika da ke gargaɗin cewa zaɓin Buhari na iya haifar da barazana ga jam’iyyar da shugabancinta.
Akwai kuma wasu rahotanni da ke nuna cewa ba a iya cimma matsaya a taron da gwamnonin suka yi a daren Talata kan yin sulhu a zabin marawa mutum guda, wanda shugaba Buhari ke so.
A wannan Talatar da ake saran kwamitin da ya tantace masu neman tikitin shugaban kasa a APC, ya gabatar da rahoton da ya tattara ga shugaban jam’iyya, Abdullahi Adamu.
‘Yan Najeriya dai na dako domin sannin abin da APC za ta tsayar kan ɗan takararta da kuma mutumin da zai yi gogayya da ɗan takarar da babban jam’iyyar adawa ta PDP ta tsayar.