Sabon Rikici ya kunno kai cikin jam’iyyar APC

Date:

Sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar APC mai mulki bayan mutum biyu daga cikin kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya bukaci sauran mambobin kwamitin su bijirewa shugabancin Sanata Abdullahi Adamu.

A wata sanarwa da suka fitar jiya Talata, mataimakin shugaban kwamitin shiyyar arewa maso yamma, Salihu Mohammed Lukman da takwaransa na kudu maso yamma, Isaac Kekemeke sun gargadi Sanata Adamu kan yanke hukuncin bai-daya da sunan shugaba kasa, Muhammadu Buhari.

Jaridun Najeriya na rawaito cewa an dage taron kwamitin har sau biyu ba tare da bayyana dalili ba ana tsaka da danbarwar siyasa.

Wadannan kananan rigingimun cikin gida na zuwa ne adaidai lokacin da ake dakon mutumin da zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar zai tabbatar a matsayin ɗan takarar shugaban kasa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...