Daga Sidi Ibrahim Jega
Zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC na Ƴan takara Gwamnan jahar Kebbi, ya kammala.
An-fafa-ta tsakanin ƴan takara guda ukku, Waɗanda dukkanin su sun Cika dukkanin ka’idojin jam’iyyar APC.
Wakilin Kadaura24 dake Jihar Kebbi Sidi Ibrahim Jega ya rawaito mana cewa an gudanar da zaben fidda gwanin Cikin kwanciyar hankali da lumana.
gasunayensu tare da sakamakon Ƙuri’un da aka samu ga wannan zaɓen da aka kammala.
Jimilla Ƙuri’un da aka yi zaɓe= 1090.
(1) Dr, Nasiru Idris (Ƙauran Malam Abdullahin Gwandu) =1055
(2) Alh. Abubakar Gari malam (shettiman Gwandu) =35
(3) Dr, Yahaya (malamawan kabi) =0
In da Dr, Nasiru Idris (Ƙauran Malam Abdullahin Gwandu) yayi nasara lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC na jahar Kebbi, da gagarumin rinjaye.
Jihar kebbi dai na daga cikin jihohin da suka kammala zaɓen fidda gwanin akan lokaci sabanin Kano Kaduna da dai sauran jihohi da har yanzu basu ma kai ga fara kada kuri’unba.