Daga Halima Musa Abubakar
Gwamnatin jihar Kano ta fayyace cewa abun fashewar da ya fashe a safiyar Talata a unguwar Sabon Gari makaranta ba’a Makaranta abun ya faru ba.
Kwamishinan yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba Cikin Wata sanarwa da ya aikowa Kadaura24, ya ce lamarin ya faru ne a wani kantin sayar da abibcin dabbobi wanda yake daura da wata makarantar da ke kan titin Aba, a unguwar Sabon Gari dake karamar hukumar Fagge.
Ya ce duk da dai har yanzu ba’a gama tantance musabbabin fashewar abun da barnar da ya yi a hukumance ba, tuni aka fara gudanar da bincike don gano musabbabin fashewar, da asarar da ya haifar da kuma matakan da ya kamata a dauka.
Malam Garba ya yi kira ga al’ummar jihar musamman mazauna yankin da lamarin ya faru da su kwantar da hankulansu, yayin da gwamnati tare da hadin gwiwar hukumomin da abin ya shafa ke ci gaba da gudanar da aikin.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa gwamnati za ta sanar da jama’a kan duk wani ci gaba da aka samu tare da gargadin mutane da su daina yada labaran da ba su da tushe balantana makama.

