Daga Rukayya Abdullahi Maida
Sanatan kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ya dakatar da taron da yayi niyar gudanawa a Wannan nara ta asabar.
Kadaura24 ta rawaito a dai taron na yau ne aka tsammaci Sanatan zai bayyana makomarsa a Siyasar Jihar Kano ko ya zauna a APC ko kuma ya fice daga Jam’iyyar.
Cikin wata Sanarwa da daraktan kula da Kafafen sada Zumunta na Gidan Shekarau Isama’il Lamido ya Fitar ta bayyana cewa an fasa gudanar da taron saboda wasu dalilai da bai bayyana ba.
“An dage Taron da aka shirya yi yau asabar a gidan H.E Mal Ibrahim Shekarau za a sanar da Ranar da Taron zai kasance insha Allah nan gaba kadan”. Inji Isama’il Lamido
Sai dai Sanarwa ta ce dage taron bashi da nasaba da Sulhun da jam’iyyar APC take So ayi da Sanata Shekarau.
“Akwai muhimman abubuwa da Ake karasa shirya wa tsakanin Manyan jagororin da zasu hadu Don ceto Kano Wato Madugu Uban tafiya da Malam Mai ta annabi”. Inji Lamido
Sanarwar dai ta tace anan gaba kadan za’a sanar da wata ranar yin taron.
Yanzu haka dai Rahotannin da suke zuwar mana sun tabbatar da fasa wancan taro , Inda tuni magoya bayan Sardaunan Kano suka Cika unguwar munduba Amma Kuma an hana su shiga cikin Gidan na Shekarau.
Da yawa daga cikin mahalatta wancan taro sun tsinci kawunansu cikin zullumin ko fasa taron yana da nasa ba da ziyarar da Gwamna Ganduje ya kaiwa Sardaunan a jiya Juma’a.