Rikicin APC: Shugaban ma’aikatan fadar Gwamnatin Kano da jiga-jigan siyasar yankinsa sun fice daga APC

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida
 Shugaban ma’aikatan fadar Gwamnatin Kano Dr. Ali Haruna Makoɗa ya fice daga Jam’iyyar APC a daren Juma’ar data gabata.
Dr. Ali makodan sun fice daga APC ne tare da Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Ɗanbatta da Makoɗa Badamasi Ayuba Ɗanbatta sai Ɗan majalisar jiha na Ɗanbatta Alhaji Murtala Musa Kore da Shugaban ƙaramar hukumar Ɗanbatta Alhaji Muhammad Abdullahi Kore sai Shugaban ƙaramar hukumar Makoɗa Alhaji Mamuda, da Shugaban jam’iyyar APC na Ɗanbatta Alhaji Musa Sansan da kuma Shugaban matasan jam’iyyar APC na Kano ta Arewa Najib Abdussalam .
Kuma tuni tun a daren jiyan suka gana da tsohon Gwamnan Kano Dr. Rabi’u Kwankwaso yanzu haka a gidansa da ke Miller Road, domin komawa jam’iyyar NNPP Mai kayan marmari.
Wannan dai na zuwa ne bayan da tsagin gwamnatin kano ta bayyana matsayarta Kan Wanda Zai yi takarar dan majalisar tarayyya a yankin Danbatta da makoda yayin da aka ce Shugaban Majalisar dokokin ta jihar kano Engr. Hamisu Ibrahim chidari.
Rahotannin da Kadaura24 ta Samu na cewa wannan kusan shi ne karon Farko da Wani ya bar APC da takawagar Mutane Masu mukamai inda Shugaban Ma’aikatar ya tafi dan Majalisar tarayyya dana Jihar da Shugabannin Kananan Hukumomi da Shugabanni a jam’iyyar APCn yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...