Daga Sani Danbala Gwarzo
Dan Majalisar dokokin Jihar Kano dake wakilar Karamar Hukumar dawakin kudu Hon. Mu’azzam El-yakub yace babu wani dan majalisa da yayi abinda yayi ya yankinsa ta fuskar ciyar da ilimi gaba.
Dan Majalisar ya bayyana hakan ne cikin wata ganawa ta musamman da yayi da wakilin Kadaura24.
wakilin yace duk da babu wani Dan majalisa da yayi abinda nayi na ciyadda ilimi gaba a yankin karamar hukumar dawakin tofa,jawabin hakan ya fito ne daga zababban Dan majalissa mai wakiltar karamar hukumar dawakin kudu a zauran majalisar dokokin jahar Kano hon muazzam el yakub.
wakilin yace duk da matsi da nuna wariya da suke fuskanta a majalisar kasancewar su na ‘yan jam’iyyar a dawa, yace hakan bai hana su yi wa al’ummar yankin su aiyukan more rayuwa ba.
mu’azzam el yakub, yace hakika ya dauki wani salo irin na jagoran darikar Kwankwasiyya na duniya Engr. Rabiu Musa kwankwaso, na tallafawa harkokin ilimi hakan ne yasa shekarar farko a zaman sa wakilin dawakin kudu ya dauki nauyin mutum tamanin da uku zuwa manyan makarantu daga sassa da ban daban na kasar nan Dan cigaba da habaka harkokin ilimi a yankin.
sannan ya bayyana farin cikin sa da godiyar sa ga mahalicci bisa yadda al’ummar Kano su ka fahimci tafiyar mai gidan sa Sanata Rabiu musa kwankwaso suna ta dafifi wajen komawa jamiyar NNPP mai alamar kayan dadi.
Dan majalisar muazzam El- Yakub ya yi Kira ga daukacin al’umma dasu cigaba da basu cikakken hadin kai da goyon baya domin su cigaba da bujuro da sabbin aikace aikacen raya kasa.