Daga Halima Musa Abubakar
Fadar shugaban kasa ta shiga cikin rikicin da ke faruwa a jam’iyyar APC reshen Jihar Kano tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.
Wata majiya mai tushe ta ce fadar shugaban kasa ta aiko da jirgin sama a daren Juma’ar nan daga Abuja zuwa Kano domin kai Ganduje da Shekarau fadar Shugaban kasa don gudanar da wani taron gaggawa na sasanta rikicin.
Taron sulhun dai an ce wani babban yunkuri ne na shirin dakile shirin sauya shekar Malam Shekarau zuwa sabuwar jam’iyyar NNPP Mai kayan marmari.
Jam’iyyar NNPP na karkashin jagorancin tsohon gwamnan Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Manyan jiga-jigan jam’iyyar APC da jam’iyyar adawa ta PDP sun shiga jam’iyyar kuma ana sa ran Shekarau a hukumance zai sanar da sauya sheka zuwa jam’iyyar a ranar Asabar din nan Mai zuwa.
Sai dai da yammacin ranar Juma’a, Gwamna Ganduje ya ziyarci tsohon gwamnan a gidansa da ke Mudunbawa Kano, a wani mataki da dakatar da Shekaran Daga barin jam’iyyar yan awanni gabanin Sanar da ficewar Shekaran daga APC Kamar yadda majiyoyi daga mundubar suka tabbatar.
Majiyoyi sun ce bayan ganawar ta sirri ne suka fara shirin tashi zuwa Abuja, Wanda dama ana ganin Wannan ne abun daya kai Ganduje gidan Malam Shekarau a daren yau.
Rahotannin da Kadaura24 ta Samu sun nuna cewa da misalin karfe 1 na daren Juma’ar nan ne Shekarau da Ganduje zasu gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari don magance Rikicin.
Kuma an ce tuni Shekarau ya Amince Zai amsa gayyatar ta Shugaban kasa, Amma dai yanzu abun a jira shi ne wannen Matakin Shekarau Zai dauka a gobe Asabar da ya kirawo taron magoya bayansa bayan gama Jin ra’ayoyin su na a zauna a APC ko a chanza Jam’iyyar?.
