Daga Barira Jamil Isa
Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi murabus daga mukaminsa
Amaechi ya yi murabus daga mukaminsa ne biyo bayan umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar na cewa dukkan mambobin majalisar ministocin da ke neman mukamai a zaben 2023, su yi murabus kafin ranar 16 ga watan Mayu.
Buhari ne ya bayyana hakan ne yayin taron Majalisar Zartarwar ta kasa.
Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito Rotimi Ameachi na daga cikin na gaba-gaba Cikin Masu neman takarar Shugabancin Kasar nan a jam’iyyar APC.