Wasu ‘yan majalisar dokokin jihar guda uku sun sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP daga APC .
Hakan na kunshe ne a cikin wasikar sauya shekar da suka aike wa kakakin majalisar dokokin jihar Kano, inda suka sanar da majalisar sauya shekar su daga jam’iyyar APC zuwa NNPP.
A cikin sanarwar da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Majalisar Dokokin Jihar Kano Uba Abdullahi ya rabawa Manema labarai, ya ce wasikun Masu dauke da kwanan watan 5/5/2022 kuma Majalisar ta karbe su a hukumance, a lokaci guda kuma Majalisar ta yi musu fatan alheri.
A cewar sanarwar, ‘yan majalisar da suka koma jam’iyyar NNPP su ne;
1. Hon Abdullahi Iliyasu Yaryasa Memba mai wakiltar mazabar Tudun Wada
2. Hon. Muhd Bello Butu,
Memba, mai wakiltar mazabar Tofa/Rimin Gado.
3. Hon. Kabiru Yusuf Ismail
Mamba, mai wakiltar mazabar Madobi
Haka zalika tsohon Kwamishinan Ma’aikatar kasafi da tsare-tsare na Jihar Kano Alhaji Nura Muhammad Dankadai shi ma ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar NNPP.
Dankadai ya bayyana ficewar tasa ne Cikin wani sako da ya aikowa Kadaura24 a yammacin Wannan rana ta laraba.