Daga Rukayya Abdullahi Maida
Rahotannin suna nuni da cewa an nada Nasir Gawuna mataimakin gwamnan Kano a matsayin wanda Zai gaji gwamna Ganduje Kar kashin tutar jam’iyyar APC a zaben gwamna na 2023.
An zabi Gawuna ne a wajen taron masu ruwa da tsaki da Gwamna Abdullahi Ganduje ya jagoranta, kamar yadda Jaridar Daily trust ta rawaito.
Kadaura24 ta kuma rawaito cewa an kuma ce masu ruwa da tsakin sun amince cewa tsohon kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Murtala Sule Garo, ya zama Mataimakin takarar Gawuna a zaben.
Rahotanni sun bayyana cewa masu ruwa da tsakin sun dauko Murtala Sule Garo ne domin a sami maslaha a jam’iyyar Kuma ta kai ga gaci cikin sauki.
Garo, wanda ake kyautata zaton shi ke da iko da tsarin jam’iyyar a matakan kananan hukumomi, ana ganin shi ne dan takarar uwargidan gwamnan, Hafsat Ganduje.