Jagoran Jam’iyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakani dangane da rikicin Jam’iyyar da Kofa
Hon. Abdulmumini Jibrin dai bai bayyana dalilinsa na ficewa daga jam’iyyar APC ba, amma majiyoyi sun ce hakan na da alaka da matakin kin ba shi tikitin komawa majalisar wakilai.
Tsakanin Jibrin da Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, na dan wani lokaci kan al’amuran siyasa na cikin gida.
Jibrin ya wakilci mazabar Kiru da Bebeji a Majalisar Wakilai a tsakanin 2011 zuwa 2019 kafin ya fadi zaben da aka sake yi a Jam’iyyar PDP. in 2020.
An rawaito cewa Asiwaju Tinubu ya tuntubi Gwamna Ganduje domin sasantawa tare da tabbatar da hadin kan Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano bai wargaje ba.
Kofa na fama da matsalolin cikin gida da mazabarsa, Amma ana ganin komai zai daidaita,” kamar yadda Majiyarmu ta rawaito
A Sanarwar da kofa ya Fitar yace yayi a Yau lahadi Zai baiyana Sabuwar jam’iyyar da zai koma, Amma watakila Sami chanji Sakamakon wannann cigaba da aka samu na Sanya baki ga jagoran jam’iyyar APC na kasa.