Daga Halima Musa Abubakar
Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Sanar da sauya Sunan rukunin gidaden dake unguwar Jaba dake Karamar Hukumar Ungogo Zuwa Sabon birnin Enugu Wato New Enugu City.
Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da yake Jawabi a wajen taron Kaddamar da Sabbin Shugabannin Kungiyar Yan kabilar Igbo mazauna Kano a unguwar church Road dake Kano.
Gwamnan Ganduje yace ya dau wannan matakin ne domin Kara inganta Zaman Lafiya da ake da shi a kano musamman tsakanin al’ummar Jihar kano da Kuma inyamurai mazauna Kano.
“Muna Jin dadin yadda kuke Zama Lafiya da kowa a jihar nan, Ina so in Sanar da ku cewa Kuma Yan Kano ne Saboda wasunku an haife su a Kano Wasu iyaye da kakanninku ma duk a Kano aka haifesu.” Inji Ganduje
Gwamnan ya kuma yi kira ga Sabbin Shugabannin da su Maida hankali wajen samar da Zaman Lafiya tsakanin yan kabilar Igbo da ma al’ummar Jihar Kano baki daya, Sannan Kuma ya basu kyautar Naira Miliyan 5 don inganta harkokin Kungiyar.