Daga Saminu Ibrahim magashi
Iyalan Marigayi sheikh Isyaka Rabi’u sun shirya walimar cin abinci tare da rabawa limaman da suka gabatar da sallar tarawi da tahajjud a masallatan khalifa shiekh ishaq rabi’u dake kwaryar birnin Kano kudade da Kuma kayan abinci.
Taron dai dama an saba gudanar da shi a duk lokaci irin wannan, wandaiyalan khalifan suke gudanarwa domin kara qarfin guiwa ga limaman da Kuma cigaba da ayyukan alkhairin da mahaifunnasu ya saba yi.
Limamai kimanin 100 ne suka rabauta da kyautar zunzurutun kudi har naira dubu ashirin da biyar biyar tare da buhunan shinkafa, inda ladanansu suka rabauta da naira dubu biyar biyar.
Walimar dai ta gudanane qarqashin jagorancin gwani Dr. yusuf ishaq rabi’u Wanda yai bayani amadadin iyalan khalifa ishaq rabi’u.
Anasu bangaren limaman sun bayyana farin cikinsu tare da addu’ar Allah ya jikan khalifa ya kuma sanya wanann kyautatawa da akaimusu a mizani.
Taron dai yasamu halarta duka iyalan khalifa dadai sauran muhimman mutane.