Daga Rukayya Abdullahi Maida
Yan Majalisar Dokoki 9 na Jam’iyyar Pdp a zauren Majalisar Dokoki ta Kano sun Mika takardar sauya Sheka zuwa Jam’iyyar NNPP.
Kadaura24 ta rawaito hakan na kunshe ne cikin wata Sanarwa da daraktan yakin yada labaran Majalisar dokokin Jihar Kano Uba Abdullahi ya Fitar.
Wadanda suka Mika takardar zuwa ga shugaban Majalisar Dokoki ta Kano Hon engr Hamisu Ibrahim chidari sun Bayyana Rikicin cikin Gida da Kuma Rashin takamaiman inda jam’iyyar ta sanya Gaba
Ana sa bangaren shugaban Majalisar Dokoki ta Kano engr Hamisu Ibrahim chidari yayi musu fatan alkairi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa daga cikin wadanda suka sauya Sheka zuwa Jam’iyyar ta NNPP sun Hada Da
1.Rt Hon. Isyaku Ali Danja Mai Wakiltar Karamar Hukumar Gezawa .
2.Hon. Umar Musa Gama, Dan Majalisa Mai Wakiltar Nassarawa.
3. Hon Aminu Sa’adu Ungogo, Mai Wakiltar Karamar Hukumar Ungogo.
4. Hon Lawan Hussain Chediyar ‘Yan Gurasa. Dan Majalisa Mai Wakiltar Karamar Hukumar Dala.
5. Hon. Tukur Muhd Dan Majalisa mai Wakiltar Karamar Hukumar Fagge .
6. Hon.Mu’azzam El-Yakub, Dan Majalisa Mai Wakiltar Karamar Hukumar Dawakin Kudu .
7..Hon. Garba Shehu Fammar Dan Majalisa Mai Wakiltar Kibiya .
8.. Hon. Abubakar Uba Galadima, Dan Majalisa Mai Wakiltar Bebeji .
9.. Hon Mudassir Ibrahim Zawaciki, Dan Majalisa Mai Wakiltar Kumbotso .
Dama dai an dade ana jiran Wannan Rana kasancewar an San cewa Suna Matukar biyayya ga tsohon gwamnan kano Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso .