Salihu Tanko Yakasai ya Kaddamar da takararsa ta Gwamnan Kano a jam’iyyar P R P

Date:

Daga Mubaraka Aliyu Ibrahim

Tsohon mashawarci ga Gwamnan Jihar Kano Kan harkokin yada labarai Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya Kaddamar da aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kano a wannan Rana cikin jam’iyyar P R P.

Da yake Jawabi a wajen taron Alhaji Salihu Tanko Yakasai yace ya fito takarar kujerar Gwamna kano ne domin fitar da al’ummar Jihar Kano daga cikin Mawuyacin halin da suke ciki.

Salihu Tanko Yakasai Wanda akewa lakabin Dawisu yace akwai tsare-tsare da ya tanada Waɗanda Zai gabatar Idan ya Zama gwamnan jihar kano.

” Idan Allah ya bamu damar zama gwamnan kano Zan tabbatar na yi Amfani da manufofin jam’iyyar P R P sabanin yadda mafi yawan daga cikin Shugabanni a kasar nan suke na sauka daga manufofin jam’iyyar su da aka zabe su a cikinta”. Dawisu

Yace Kowa ya shaida irin aiyukan da gwamnonin jam’iyyar P R P na baya suka gudanar a jihohin Kano da Kaduna, Inda Abubakar Rimi yayi Aikin da har yanzu ba’a Sami gwamnan da yayi aikin kamar sa ba.

Bayan na fice daga jam’iyyar APC, masoya da magoya bayana sun yi ta Kawo Shawarar mu Koma PDP da sauran jam’iyyu har ma da jam’iyyun yarabawa, Amma bayan na yi addu’a na Sami nutsuwar mu Koma jam’iyyar P R P ta Malam Aminu Kano Saboda ita ce ta Masu Gaskiya da akida”.inji Salihu Tanko Yakasai

Ya Kuma bada tabbacin zai bijiro da aiyukan da zasu ingata rayuwar al’ummar Jihar Kano ta fannoni daban-daban, domin yace hakan na daga cikin manufofin jam’iyyar data tayi fice wajen kwatowa talakawa yancin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...