Kano 2023: Inuwa Waya ya nada Dr. Jalo a Matsayin Daraktan Tuntuba na takararsa

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

Guda Cikin Yan takarar gwamnan Jihar Kano Alhaji Inuwa Waya ya nada Umar Yusuf Jalo wanda aka fi sani da Dr. Jalo a Matsayin Daraktan Tuntuba na takararsa ta Gwamna.
Kadaura24 ta rawaito da yake Mika takardar Kama Aiki ga sabon daraktan, Alhaji Inuwa Waya ya ce an baiwa jalon mukaminne duba da kwarewa da aikin tukuru da yake yi domin Samun Nasarar takarar gwamna da Inuwa Waya ke yi.
Ya Kuma bukace shi da ya zage dantse wajen sauke nauyin da aka doramasa don tabbatar da nasarar ganin Inuwa Waya ya zama gwamna Jihar Kano.
A Jawabinsa Sabon Daraktan Tuntubar Hon. Umar Yusuf Jalo ya bada tabbacin Zai yi duk Mai yiwuwa wajen samun Nasarar takarar Inuwa Waya a Shekara ta 2023.
Dr. Jalo wanda Guda ne cikin Masu Magana a radiyo a Jihar Kano yace zai shiga lungu da sako na jihar kano domin Ganin Inuwa Waya ya zama gwamna Jihar Kano a zaben Shekara ta 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dan Majalisar tarayya daga Kano ya fice daga jam’iyyar NNPP

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal, Injiniya Sagir...

Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar...

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...