Daga Aisha Gwadabe
Mahukunta a Kasar Saudiyya sun bayyana cewa sun baiwa Nigeria adadin mutune dubu 43 ne za su sauke farali a bana.
Babban sakataren hukumar Jin dadin alhazai na Kano Muhammad Abba Danbatta ne ya sanar da hakan yayin taron manema Labarai a ranar Laraba.
Muhd Danbatta ya ce hakan ya biyo bayan yadda kasar Saudiyya ta ce adadin mutune Milyan daya ne kadai za su gudanar da aikin hajjin bana a fadin duniya.
Ya ce wannan adadi da aka baiwa Najeria na da alaka da yawan mutanen da Najeria ta ke da shi.
Muhammad Danbatta ya ce ko da yake har yanzu Hukumar kula da aikin hajji ta Kasa NAHCON bata fitar da kudin aikin hajjin bana ba Amma alamu na nuna kudin zai karu fiye da yadda aka biya a shekarun baya
Ya ce a baya an canja Dala akan 350 yanzu kuma ta Kai 408 da ke nuna lallai za a samu Karin kudin.
A yanzu dai ana jiran hukumar kula da Aikin hajji ta Kasa NAHCON ta baiwa kowacce jiha adadin kujerunta tare da bayyana adadin kudin Aikin hajjin na bana.