Daga Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa
Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na Jihar Kano Alhaji Nura Mai Dankadai ya bujirewa Umarnin Gwamna Ganduje na dakatar da shi da yayi daga ajiye mukaminsa.
Hakan na kunshe ne cikin wata Sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman ga gwamanan Kano a Ma’aikatar yada labarai Abdul Umar faruk ya Sanya a Sahihin shafinsa na Facebook.
Wannan mataki da Nura Dankadai ya dauka ya nuna cewa Nuran ya Yi hakan ne domin nuna duniya cewa sai yayi takarar da ta Dan Majalisar wakilai a Kananan Hukumomin Doguwa da Tudun Wada ko da Babu goyon bayan Gwamnatin Kano.
Kadaura24 ta rawaito Dana dai Nura Muhammad Dankadai ya ajiye mukaminsa ne domin ya shiga takarar Majalisar wakilai a Kananan Hukumomin Doguwa da Tudun Wada domin Kalubaletar Hon. Alhassan Ado Doguwa.