Yanzu-Yanzu: Abdulmumini Kofa ya ajiye Mukaminsa don yin takara

Date:

Tsohon Dan Majalisar wakilai da ya wakilci Kananan Hukumomin kiru da Bebeji Abdulmumini jibril kofa ya Ajiye mukaminsa na Shugaban Hukumar Samar da gidaje ta tarayya domin ya tsaya takara Dan Majalisar wakilai.

Kadaura24 ta rawaito hakan na kunshe ne cikin wata Sanarwa da kofan ya Fitar, Inda a cikin Sanarwar ya godewa Shugaban kasa Muhammad Buhari bisa damar daya bashi na jagorantar Hukumar.

Abdulmumini Kofa Wanda shi ne Jarman Bebeji ya yabawa abokan aikin da bisa gudunmawar da suka bashi har ya jagoranci hukumar Cikin nasara.

Rahotannin sun nuna Yanzu a jam’iyyar APC Mutane uku ne zasu nemi kujerar Dan Majalisar wakilai da Zai wakilci Kananan Hukumomi Kiru da Bebeji, da shi kofan da Sanusi said Kiru da Kuma Dan Majalisar da ke kai Hon. Ali Datti Yako.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dan Majalisar tarayya daga Kano ya fice daga jam’iyyar NNPP

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal, Injiniya Sagir...

Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar...

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...