Hukumar Hisba a K/H Garun Malam ta baiwa Marayu sama da 150 kayan sallah

Date:

Daga Safyanu Dantala Jobawa

Shugaban Karamar Hukumar Garun mallam Alhaji Mudassur Aliyu Dakasoye ya bukaci mawadata da sun rinka tallafawa marayu da sauran jama’a masu bukata ta musamman.

Kadaura24 ta rawaito Alh. Mudansur Aliyu Dakasoye ya bayyana hakan ne a wajen taron mika tallafin suturu ga marayun karamar hukumar wanda ya gudana a cibiyar yada addinin musulunci dake karamar hukumar.

Shugaban Karamar Hukumar ya yaba wa hukumar Hisba ta karamar hukumar bisa namijin kokarin da ta yi na samar da tufafi ga marayu sama da 150 Waɗanda kudinsu ya kai sama da naira dubu dari biyar da bakwai a matsayin wani dan tallafi daga gareta.

” A irin Wannan lokaci Yana da kyau mawadata da Sauran Hukumomi irin Waɗannan su Rika tallafawa marayu da masu karamin karfi har ma da masu buƙata ta musamman Saboda halin matsin rayuwa da ake Ciki a kasa baki daya”. Inji Dakasoye

Alh. Mudassur Dakasoye, ya ce Karamar Hukumar garun mallam tana iya bakin kokarin ta wajen tallafawa al’umma don rage Matsalolin da ake fama da su ma Rashi.

A nasa jawabin, tsohon shugaban karamar hukumar Alh. Sa’adu Abashe a madadin iyayen marayun, ya gode wa hukumar Hisbar karamar hukumar abisa wannan tallafin.

Wakilin jaridar Kadaura24 ya ruwaito mana cewar nan take kowanne maraya ya karbi tallafinsa daga hannun shugaban karamar hukumar tare da yin godiya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...

Na riga Kwankwaso shiga harkokin Siyasa – Sanata Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jaridun Amurka sun bankado Tsare-tsare uku da sojojin Amurka ke yi don tunkarar Najeriya

Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar...

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...