Daga Rukayya Abdullahi Maida
Karin Kwamishinoni Guda biyu sun sauka daga mukaminsu a wannan rana ta asabar.
Kadaura24 ta rawaito Mukhtar Ishaq Yakasai Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka na Musamman na Jihar Kano da Alhaji Ibrahim Ahmad Karaye Kwamishinan Ma’aikatar yawon Bude idanu ta Jihar Kano sun ajiye mukaminsu domin yin takarar Majalisar Tarayya .
Muntari Ishaq Yakasai Zai tsaya ne takarar Majalisar tarayyya mai Wakiltar Karamar Hukumar Birni, Yayin da shi kuma Ibrahim Ahmad zai yi takarar Majalisar tarayyya a Kananan Hukumomin Karaye da rogo.
Yanzu haka dai Kwamishinoni 5 kenan suka ajiye mukaminsu a Wannan rana Sakamakon Umarnin da Gwamna Ganduje ya bayar a daren jiya.