Hukumar kula da gasar firimiya ta Najeriya, Nigeria Professional Football League (NPFL), ta bai wa ƙungiyar ƙwallon kafa ta Kano Pillars damar ci gaba da buga wasanni a filin wasanta na Sani Abacha da ke Kano.
Wata sanarwa da hukumar ta aike wa kulob ɗin ta ce an ba shi damar ce bayan duba na tsanaki.
Hukumar ta ce wajibi ne Kano Pillars ta tanadi wani filin wasan da za ta ci gaba da buga wasanni da zarar an fara aikin gyara ciyawar filin taka leda ta filin kafin kammala shi.
Pillars ta ce ta amince da sharaɗin, har ma ta ce za ta buga wasanta na gaba tare da Katsina United a gida Kano ranar 16 ga watan Afrilu.
Pillars ba ta buga wasa a gida ba a kakar bana sakamakon matakin da NPFL ta ɗauka, inda ta umarci a sauya ciyawar filin taka ledar.
Yanzu haka Pillars na mataki na 13 da maki 26 bayan buga wasa 22 a kakar bana ta 2022/23.