Bincike: Musulmi za su yi azumi har sau biyu a shekarar 2030

Date:

 

Masu ilmin taurari sun ce a shekarar 2030 mai zuwa, Musulmin duniya za su yi azumin watan Ramadan har sau biyu.

BBC Hausa ta rawaito Masanan sun ce watan Ramadana zai bayyana har sau biyu a cikin shekarar – na farko a watan Janairu, na biyu kuma zai bayyana ne a karshen watan Disambar shekarar, yanayin da tun 1997 ba a taba gamuwa da shi ba.

Babban dalilin aukuwar haka shi ne bambancin da ke tsakanin shekarar Musulunci da ake lissaftawa da bayyanar wata, da kuma shekarar nasara wadda aka danganta da kwanakin da duniya ke dauka kafin ta zagaya rana.

Sannan wannan yanayin a aukuwa ne sau daya cikin shekara 30 saboda shekarar Hijira ba ta kai tsawon ta nasara da kwanaki 11 ba, kamar yadda Khaled al-Zaqaq, wani mai nazarin taurari dan kasar Saudiyya ya bayyana a Twitter.

Tsawon shekara guda ta Hijira kwana 354 ne, inda shekarar nasara kuwa ke da kwana 365.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...