Gwamnatin tarayyya na tattauna da ASUU kan yajin aiki

Date:

Gwamnatin tarayyya ta hannu Ministan Kwadago da Ayyuka, Chris Ngige, na ganawa da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa wato ASUU, a yau Litinin.

Jaridar Punch ta rawaito cewa ana ganawar ne da yammacin yau Litinin tsakanin wakilan gwamnati da na ASUUn.

Kwanaki 56 kenan da ASUU ta shiga yajin aiki a Najeriya sakamakon abin da ta bayyana gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami’a na kasar.

BBC Hausa ta rawaito ASUU dai na ganin yajin aikin ne hanyar karshe da take bi domin tilasta wa gwamnatin Najeriya biya mata bukatunta.

Yajin aikin malamai a Najeriya ya fi yin tasiri a kan dalibai wadanda ke tsintar kansu cikin damuwa, dalilin da ya sa wasu ke ganin ya kamata kungiyar ta sauya salon tunkarar rikicinta da gwamnatin kasar ba sai lallai ta hanyar yajin aiki ba.

Wasu bayanai sun nuna cewa kungiyar ta ASUU ta daka yajin aiki sau 15 tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokuradiyya a 1999, lamarin da kan jefa harkokin karatu cikin mawuyacin hali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...