Zamu cigaba da hada kai da kungiyoyin bada tallafi don inganta Rayuwar al’ummarmu – Gwamnan Gombe

Date:

DAGA MUSBAHU BALA CHEDIYAR YAN GURASA

Gwamnan jahar Gombe, Muhammad Inuwa yahya ya jadda kudurin gwamnatinsa na jawo kungiyoyin bada tallafi na duniya don bunkasa rayuwar Al’ummar jahar.

Gwamna Inuwa yahya na ya bayyana hakan ne a yayin da yake kaddamar tallafin kayyakin sana’o’i ga masu bukata ta musamman,Wanda Gwamnatin da hadin gwiwar cibiyar Samar da tallafin Jin kai ga Al’umma ta Qatar foundation suka Gudanar.

Gwamnan yace daya daga manyan manufofin gwamnatin sa shi ne bunkasa rayuwar mutane masu bunkata ta musamman don kyautata Rayuwar su.

Ya kuma zayyano ire-iren kayan tallafin da suka bayar, da suka hadar da Keken guragu da keken dinki da Babura masu kafa uku da injin markade da kuma sandu na musamman na zamani masu tallafawa masu larurar gani.

Ya kuma Yi kira ga wadannan suka Amfana suyi kyakkawan amfani da abun da suka samu.

Ansa jawabin babban daraktan cibiyar Qatar foundation a Nigeria, Hamdi assayyid Muhammad Abdallah, yace hadin kai da suke samu daga wurin gwamnatin jahar, shi ne abun da ya basu kwarin gwiwar zuwa gombe da cigaba da kawo ayyukan alheri, domin duk tsarin da suka zowa da gwamnan na hahadaka yana cikawa ya kuma godewa gwamnatin bisa Basu filin da tayi din ginin asibiti, makaranta,da kuma masallaci,harma da wurin shakatawa domin masu bukata ta musamman.

Shi ma a nasa jawabin shugaban kungiyar masu bakata ta musamman na jahar Dr. Isiyaku, ya godewa gwamnatin jahar Gombe bisa irin kulawar ga masu bukata ta musamman.

Daga Bisani dai gwamnatin ya jagoracin yan tawagarsa da yan cibiyar ta Qatar foundation zuwa inda aka tanada domin wadannan ayyukan,tare tare da aza harsashin ginin Wanda ake sa ran kammalashi cikin watanni 12.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...