Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi barazanar cewa shi da sauran gwamnonin yankin za su ɗauki sojojin haya don kare rayukan mutanensu idan gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaba Buhari ta kasa kawo ƙarshen hare-haren ‘yan fashi a yankin.
Da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan ya gana da Buharin a ranar Juma’a, El-Rufai ya ce ba ‘yan fashin daji ne suka kai hari kan jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Abuja ba – “yan Boko Haram ne”.
“Na faɗa wa shugaban ƙasa cewa wallahi idan ba a ɗauki mataki ba wannan abin ba zai tafi ba…dole sai dai mu gwamnoni mu ɗauki mataki don kare rayukan al’ummarmu,” in ji shi.
“Ko da hakan na nufin ɗaukar sojojin haya don su zo su yi aikin, za mu yi hakan don kawo ƙarshen lamarin.”
Sai dai gwamnan ya ce shugaban ƙasa ya faɗa masa cewa gwamnati za ta ɗauki matakin daƙile hare-haren a watanni masu zuwa.
Wasu rahotanni sun sha zargin cewa gwamnatin Najeriya ƙarƙashin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ta ɗauki sojojin haya don yaƙar Boko Haram a arewa maso gabas, amma babu tabbas game da rahoton saboda gwamnatin ba ta taɓa bayyana haka ba.
Harin da ‘yan bindigar suka kai kan jirgin ƙasa a yammacin Litinin da ta gabata ya yi sanadiyyar mutuwar mutum aƙalla takwas tare da raunata kusan 40. Har yanzu ba a tantance yawan waɗanda suka yi garkuwa da su ba