Daga Mubaraka Aliyu Abubakar
Kwamitin gudanarwa na masallacin ya dakatar da babban limamin masallacin Juma’a na Apo da ke Abuja, Sheikh Nuru Khalid, saboda sukar da ya yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harin bam na jirgin kasa na Kaduna.
Kadaura24 ta rawaito Limamin, a cikin hudubarsa ta Juma’a, ya soki shugaban kasa kan gazawar sa ta zuwa Kaduna don ganin Waɗanda harin ta’addancin da aka kai ya rutsa da su.
Ya ce shugaban ya je Kaduna domin yakin neman zabe, amma ya ki zuwa jihar bayan harin bam don ya jajantawa al’umma.
“Shugaban kasa Buhari yace wai yana Allah wadai, Kowa ma ai yayi Allah wadai da faruwar lamarin, in banda ‘yan ta’adda, ya kamata shugaban kasa ya ziyarci jihar domin jajantawa wadanda abin ya shafa”. Inji Malamin
Shugaban kwamitin kula da masallacin, Sai’du Dansadau, ya ce an dakatar da malamin ne saboda hudubar da yayi a ranar 1 ga Afrilu ta za iya tunzura al’umma.
Ya bayyana cewa Shehun Malamin ya yi wa’azi na hana al’umma yin abun da kundin tsarin mulkin Kasa ya basa, ta hanyar shawartar masu zabe da su baiwa siyasa sharadi kafin zaben su.
Dansadau ya kara da cewa wa’azin ya sabawa tsarin addinin Musulunci.