Daga Abdulmajid Habib Isa
Sha’aban Sharada, Shugaban Kwamiti Tsaro da Sirri na Ƙasa a Majalisar Wakilai, Sha’aban Sharada, ya baiyana cewa zai tsaya takarar gwamnan Jihar Kano a zaɓen 2023 har ma ya karɓi mulki a hannun Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar
Sharada, wanda yanke wakiltar mazaɓar Kano Municipal a Majalisar Wakilai ta Taraiya, ya baiyana hakan ne yayin bikin raba kayayyakin tallafi ga magidanta 20,000, da a ka yi a Filin Polo a Jihar Kano a yau Alhamis.
Sharada, wanda ya ke ɓangaren APC na ƴan G7, karkashin jagorancin Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce tuni ya tanadi kundin gyaran jihar idan ya karɓi mulki a hannun Ganduje.
“Mu a mulkin mu, al’umma za mu yi wa hidima idan Ganduje ya mika min ragamar mulki a 2023, sannan za mu ciyar da Kano da al’ummar ta gaba.
“Gwamnatin mu, da yardar Allah, idan Ganduje ya miƙa min kujerar mulkin Kano, zamu kai jihar nan zuwa babban matsayi na karfin tattalin arziki kamar yadda a ka san ta a da, wanda a yanzu kuma jihar ta rawa wannan matsayi.
“Za mu tafi da kowa idan zai iya bamu gudunmawa wajen farfaɗo da jihar mu Kano ko ma a ko wacce jami’ya mutum ya ke,” in ji Sharada.
A kan kayan tallafin da ya raba, Sharada ya yi bayani cewa ya raba babura 1,000, kekuna 500 da kuma keken dinki 500.
Sauran sun haɗa da injin gasa gurasa na zamani 44 ga mata goma-goma daga kowacce Ƙaramar Hukuma a cikin Ƙanan Hukumomi 44 na jihar, sai kuma akwatin kayan sana’o’in hannu 300 wanda kuɗin sa ya kai Naira miliyan 39.
Sai kuma motoci har ma da takardun ɗaukar aiki, da sauran su.


