Rahama Sadau ta bayyana yadda ta kubuta daga harin Jirgin kasa daga Abuja-Kaduna

Date:

Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman

Shahararriyar jarumar nan ta kannywood, Rahama Sadau da ‘yan uwanta sun godewa Allah da ya raya ta ta tsallake rijiya da baya, daga harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Kadaura24 ta rawaitoA daren ranar Litinin ne ‘yan ta’adda suka kai hari kan wani jirgin kasa da ya taho zuwa Kaduna, Inda suka jefa bama-bamai a kan layin dogo hakan ya tilastawa jirgin tsayawa

Shaidun gani da Ido sun ce daga baya maharan sun kewaye jirgin, inda suka bude wuta kafin daga bisani su samu shiga da karfi, inda suka yi ta harbe-harbe, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu mutane tare da jikkata Wasu.

Da take magana a Sahihin shafinta na Twitter, jarumar ta bayyana cewa an shirya za ta shiga jirgin tare da ‘yar uwarta amma suka rasa jirgin, sai dai ta bayyana cewa tana da abokai da suka shiga cikin jirgin kuma wadanda harin ya rutsa da su.

Ta rubuta, “Ni da ‘yar uwata mun so kasance a cikin jirgin da aka kai hari a daren jiya amma muka rasa shi”. MUN RASA!!

Jarumar ta yi amfani da damar wajen baiwa magoya bayanta shawarar su karbi katin zabe na dindindin (PVC) da kuma tabbatar da kirga kuri’unsu.

“Mu (AREWA) mu muka kawo kanmu wannan halin, mun zabi Shugabannin yanzu don su Magance Mana Matsalar tsaron da ta addebe mu, Amma hakan taki samuwa, to don haka idan Muka mallaki katin zabe sai mu zabi Shugabanni na gari.

A yau, an jibge jami’an tsaro masu tarin yawa a filin wasa na MKO Abiola, na fahimci cewa Nijeriya tana iya yin Maganin Wannan matsalar, kawai sun zabi su yi watsi da mu ai ta kashemu, so ba ruwan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...