Yan bindiga sun tashi Bom a jirgin kasan Kaduna-Abuja da ke dauke da fasinjoji 970

Date:

Rahotanni sun ce wasu ƴan bindiga sun tayar da bam a titin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna da ke ɗauke da fasinja 970.

Rahotanni sun ce maharan sun yi nasarar hana jirgin tafiya, inda suka buɗe wuta.

Ɗaya daga cikin fasinjan da ke cikin jirgin ya tabbatar wa BBC da harin, inda ya ce maharan sun kwashi mutane sun tafi da su. Sannan jami’an tsaron da ke cikin jirgin sun yi musayar wuta da ƴan bindigar.

Ya ce sun kashe mutum guda. “Mun ji ƙarar harbe harbe, muna cikin tashin hankali,” in ji shi.

Wani ma’aikacin tashar jirgin a Rigasa ya shaida wa BBC cewa “jirgin ya kamata ya iso misalin ƙarfe 8:20 amma har yanzu ba labari.”

Hukumomin sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya da hukumomin gwamnatin Kaduna ba su tabbatar da al’amarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...