Yan sanda sun mamaye gidan Muhuyi Rimingado dake Kano

Date:

Daga Sayyadi Abubakar

A jiya da yammacin Lahadi ne dai a ke zargin cewa jami’an ƴan sanda a Jihar Kano sun mamaye gidan tsohon Shugaban Hukumar Ƙorafe-ƙorafen jama’a da Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, Muhuyi Magaji Rimingado.

A watan Yulin bara ne a ka dakatar da Rimingado bayan da ya fara binciken zargin badaƙala da aringizon kuɗaɗen kwangiloli da a ke zargin da hannun iyalin gwamna a ciki.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta jiyo cewa ƴan sandan sun girke motocin su a kofar gidan Rimingado da ke kan titin Yahaya Gusau, inda da ga bisani su ka dirar masa da misalin ƙarfe 7 na yamma.

Mazauna unguwar sun tabbatar da mamaye gidan Rimingado da ƴan sanda su ka yi ga DAILY NIGERIAN, inda su ka ce sun ji ƙarar harbe-harbe yayin da ƴan sandan ke ƙoƙarin kama shi.

Mazauna unguwar sun ƙara da cewa bayan sun ji ƙarar harbe-harben da misalin ƙarfe 7 na yamma, da misalin 9:30 na yamma sai kuma a ka ga motocin su na cin taya yayin da su ka bi wata mota da ta fito da ga gidan Rimingado.

Jaridar ba ta samu tabbacin ko ƴan sandan sun cafke Rimingado a yayin sintirin ba.

Da a ka tambayi kakakin rundunar yan sanda ta Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ba a bashi bayani a kan lamarin ba, inda ya yi alkawarin zai bincika.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...