Yan Sanda a Kano sun yi watsi da batun yajin aikin da wasun su sukai niyyar yi

Date:

Daga Aisha Aliyu
jami’an ‘yan sandan Najeriya a kano sun yi biyayya ga kiran da IGP ya yi musu na yin watsi da yajin aikin da wasu jami’an suka yi niyyar yi.
 Kadaura24 ta rawaito da yake zantawa da manema labarai a Kano kwamishinan ‘yan sandan Sama’ila Shu’aibu Dikko ya ce ya ziyarci dukkanin jami’an ‘yan sanda da ke cikin birnin Kano, kuma duk jami’an sun halacci wuraren aikinsu yadda ya kamata.
 “Mu ’yan kishin kasa ne na gaske, kuma ba za mu taba shiga yajin aikin da aka ce za mu yi ba, yau Asabar jami’anmu sun fito sanye da kakinsu, mu yan sanda ne kuma muna biyayya ga manyan mu”.
 Sama’ila Shuaibu Dikko ya kara da cewa, ‘yan sanda sun san irin namijin kokarin da Sufeto Janar na ‘yan sandan ya yi wajen kyautata jin dadin jami’ansa manya da kanana don haka za su ba da dukkan goyon bayan da ya dace ga shugabancinsa don ya cimma manufofin da ya sanya a gaba.
 “Ba mu da niyyar zuwa yajin aiki, mu Jami’an tsaro ne, kuma mun san muna cikin dakarun rundunonin ba sa yajin aikin, don haka duk wanda ya yi hakan tamkar ya so yin zagon kasa ne”. Inji CP Dikko
 Shuaibu Sama’ila Dikko ya bukaci jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya da su kara himma da kwazo wajen gudanar da ayyukansu, domin kare rayuka da dukiyoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...

Na riga Kwankwaso shiga harkokin Siyasa – Sanata Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jaridun Amurka sun bankado Tsare-tsare uku da sojojin Amurka ke yi don tunkarar Najeriya

Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar...

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...