Da tsaftar Muhalli ne kadai za mu yaki cututtuka da dumamar yanayi a Nigeria – Falakin Shinkafi

Date:

Daga Sayyadi Abubakar Gwagwarwa

Dan kishin kasar nan Falakin Shinkafi Amb. Yunusa Yusuf Hamza ya bayyana tsaftar Muhalli da cewa hanyace ta inganta Lafiyar al’umma da Kuma gojewa dumamar yanayi.

Kadaura24 ta rawaito Falakin Shinkafin ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da wakilin Kadaura24 a unguwar Yakasai dake Karamar Hukumar birni a jihar kano.

Yace tsaftar Muhalli wajibi ce ga al’umma, matukar suna buƙatar gujewa yaduwar cututtuka Waɗanda suke hallakawa ko jikkata al’umma, Inda ya ce rashin tsaftar Muhalli Kan jawo cututtuka a cikin al’umma Waɗanda ake rasa musabbabin yaduwar su.

Idan al’umma Suna tsaftace Muhalli su za a Sami sauki wajen yakar cututtuka da matsalar dumamar yanayi da a yanzu haka ake fama da ita ko’ina a duniya”. Inji Amb. Yunusa Yusuf

Yace ” Idan har kasashen da suka cigaba, a kullum zasu Rika Neman Hanyar da zasu yaki dumamar yanayi, to Babu shakka mu kuwa kamata yayi mu tunkari matsalar tun daga tushe, tunda dai bamu kai su ba karfin tattalin arziki ba”. Inji Falakin Shinkafi

Amb. Yunusa Yusuf Hamza ya ce ya shiga an yi aikin tsafar muhalli na Karshen wata ne domin nuna muhimmancin hakan ga sauran al’umma Musamman Matasa da Sauran al’umma.

Yayi fatan masu ruwa da tsaki a Cikin al’umma zasu rika shiga harkokin cigaban al’ummar su domin yin hakan zai baiwa yan baya damar yin koyi da abubuwan alkhairi da suka ga manyansu Suna yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...