Daga Rabi’u Usman
Sarkin Kabilar Kanuri mazauna jihar kano Alhaji Mustapha Lawan, kuma Wakilin Shehun Borno a jihar Kano ya kai ziyarar neman Goyon bayan Malamai a nan kano musamman wajen rawar da suke takawa wajen taimakawa da Addu’oin neman zaman lafiya a jihar Kano dama kasa baki daya.
Sarkin Kanurin ya kai ziyara ne ga Babban Limamin masallacin Murtala Sheikh Malam Badamasi Dan Taura, inda ya nemi Limamin daya karfafawa Jama’a gwiwa wajen yin Addu’a ga shugabanni da kuma zaman lafiya, tare da kwanciyar hankali harma da hada kan kabilar kanuri a nan kano domin zama tare a matsayin kasa daya Al’umma daya.
Yana mai cewar, akwai kyakkyawan Alaka tsakanin malaman jihar kano da kasar Borno kamar yadda tarihi ya nuna tun a baya, musamman ta fannin cinikayya da mutanen Borno ke shigowa kano, yayin da su kuma mutanen kano suke zuwa borno neman ilimi.
A nasa bangaren Babban Limamin Masallacin Murtala Malam Badamasi Dan Taura ya Jaddada Goyon Bayan sa ga sarkin da kuma tabbatar dayin Addu’a ga jihar kano dama kasa baki daya.
Yana mai cewar, ta haka ne za’a samar da shugabanni na gari da zasu jagoranci Al’ummar jihohi dama kasa baki daya.