Jam’iyyar APC zata kara bunkasa bayan babban taron ta na Kasa – Ganduje

Date:

Daga Sayyadi Abubakar Sadeeq

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa jam’iyyar APC zata kara bunkasa bayan kammala babban taron ta na kasa, Wanda za a gudanar a gobe asabar 26 ga watan Maris din nan.

Kadaura24 ta rawaito Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da Manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.
Gwamnan wanda shi ne Shugaban Kwamitin tsare-tsare na taron jam’iyyar, yace Matsalolin rashin fahimta da ake samu a jam’iyyar ta APC musamman game da Shugabancin jam’iyyar a matakin kasa, babu wani nakasu ko rarrabuwar kawuna da za’a samu bayan taron.
Yace jam’iyyar APC ita ce jam’iyya mafi girma yanzu a Africa, kuma yana da yakinin zata sake kafa gwamnati a matakai daban-daban a Ƙasar nan a Shekara ta 2023.
Tun lokaci da aka kafa jam’iyyar APC muna Samar da Shugabannin mu ta hanyar masalaha, Kuma Bamu taba Samun matsala ba don haka a wannan karon ma Ina baka tabbacin ba zamu Sami wata matsala ba “. Inii Ganduje
 Ganduje ya Kara da cewa Matakin yin masalaha ga yan takara da jam’iyyar ta ke yi shi ne yake kara mata girma, kuma yace matsayinsu na masu ruwa da tsaki a jam’iyyar, zasu cigaba da tattaunawa domin shawo kan  Waɗanda suka ki yarda da masalaha a zaben da za a gudanar gobe.
” Matakin da shugaban kasa Muhd Buhari ya dauka na kokarin ganin anyi maslaha abun ne da ya dace Kuma hakaan zai Kara hada Kan ‘ya’yan jam’iyyar APC a kasa baki daya”. Inji Ganduje
Al’umma da yawa dai Suna ganin jam’iyyar APC zata iya shiga rudani bayan babban tsaron ta na kasa, Saboda yadda aka kasa Samun maslaha a tsakanin yan takarar Shugabancin jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...