Wani Limamin Masallacin Juma’a ya ajiye limanci sabo da zai tsaya takara a Katsina

Date:

 

Imam Muhammad Hashim, Limamin Babban Masallacin Juma’a na GRA a Jihar Katsina ya ajiye muƙamin limancin sabo da zai tsaya takara.

A wasiƙar ajiye limancin da ya rubuta, mai ɗauke da kwanan watan 24 ga Maris, Mallam Hashim ya yi addu’ar Allah Ya rubuta masa ayyukan alherin da ya yi a cikin ayyukansa.

Wani ɓangare na wasiƙar, wacce Kadaura24 ta gani ya ce, ” Ni Muhammad Hashim (Liman) na ake muƙami na na limancin Babban Masallacin Juma’a na GRA sabo da tsaya wa takara da zan yi.

“Ina fatan Allah SWT Ya rubuta mana ayyukan mu na alheri a cikin ibadun mu da mu ka gabatar, Ya yafe mana kusa-kuren mu Amin.

A cikin wasiƙar, mai ɗauke da sa hannunsa, Hashim ya nemi yafiyar ƴan kwamitin masallacin da ma al’umma baki ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar...

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...