Ku Gina kyakykyawar alaka da juna don hadin kan Kasa – DG NYSC ga ‘yan hidimar kasa

Date:

Daga Sayyadi Abubakar Gwagwarwa

Babban Darakta na Hukumar Kula da yan yiwa kasa hidima na Kasa, Manjo Janar Shu’aibu Ibrahim, ya bukaci Matasa masu yiwa kasa hidima da su yi kyakykyawar alaka da nuna domin gina kasar nan.

Kadaura24 ta rawaito Janar Shu’aibu Ibrahim ya bayyana hakan ne a yayin bikin rantsar da Matasan rukunin A kashi na 2 na shekarar 2022 a Kano wanda aka gudanar a sansanin ‘yan yiwa kasa hidima dake Kusalla, karamar hukumar Karaye a jihar Kano.

Darakta Janar wanda ya samu wakilcin ko’odinetar shirin a Kano Hajiya Aisha Tata Mohammad ta ce an Samar da shirin ne domin hada matasa da suka fito daga bangarori daban-daban a wuri guda ba tare da la’akari da banbancin, addini ko al’ada ba sai don hade kan al’ummar kasar nan.

Ya ce shirin na NYSC zai bai wa matasan damar samun yanayi mai kyau don ba da gudummawar su yadda ya kamata domin gina Nigeria.

Janar Shu’aibu Ibrahim ya karfafawa matasan gwiwar yin koyi da dabi’ar kishin kasa da sadaukar da kai, da nufin bunkasa hadin kai da zaman lafiya a kasa.

Shugaban hukumar ta NYSC ya bukaci sabbin yan yiwa kasa hidimar da aka rantsar da su tabbatar da cewa sun yi amfani da sana’o’in da aka koya musu don su zamo masu dogaro da kawunan.

A nata jawabin, Babbar jami’ar shirin NYSC ta Jihar Kano Hajiya Aisha tata Muhammad wadda ta samu wakilcin Daraktan sansanin Isa Isiaka ta ce an yi wa matasa 1751 rijista da suka hada da maza 961 da mata 790.

Aisha Tata Mohammad ta gargade su da su guji shiga ayyukan daba, shaye-shayen miyagun kwayoyi, da sauran abubuwan da basu dace ba.

Ta kara da cewa sansanin na kano cike yake da bin ka’idar kariyar Covid-19.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...