Kotu ta sassauta sharuɗɗan belin Danbilki kwamandal

Date:

Daga Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa
Kotun Majistare ta jihar Kano mai lamba 58 karkashin jagorancin Aminu Gabari a ranar Alhamis ta yi nazari kan sharuddan belin da ta aiyana a baya kan Abdulmajid Sani Kwamanda.
 Kadaura24 ta rawaito hakan ta faru ne Sakamakon rokon da lauyan Abdulmajid Danbilki kwamanda Barista Tajuddeen Funsho yayi a gaban kotun.
Da yake gabatar da koron, Barr. Funsho ya bukaci kotun da ta sake duba sharuddan da ta gindaya a baya a kan wanda yake karewa, inda ya ce wanda ake kara zai ci gaba da zuwa kotu domin sauraren laifukan da ake kararsa akan su Waɗanda suka shafi bata sunan gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
 A martanin da ya mayar, lauyan masu shigar da kara, Barr. Wada Ahmad Wada, ya ce batun sake duba belin kotu ce ta yanke hukunci, inda ya yi fatan za a bi ka’idojinshari’a da adalci wajen sake nazarin.
 A hukuncin da ya yanke, Alkalin kotun ya umurci Danbilki da ya gabatar da mutane 2 wadanda suka hada da: mahaifinsa ko wakilinsa, maimakon Wakilin Gabas na masarautar Kano da aka bukata tun da farki.
 Hakazalika, kotun ta umurci wanda ake kara da ya gabatar da limamin duk wani masallaci da ke unguwar Koki, ko kuma limamin kowane masallacin da ya ke gudanar da sallarsa a wajen.
 Mai Shari’a Gabari ya kuma ba da umarnin cewa, haka nan wanda ake tuhuma zai iya kiran duk wani shugaban addini a cikin al’umma, idan har bai samu wani Imami da zai tsaya masa ba.
 Wannan ya maye gurbin Babban Limamin Masallacin hajiya Mariya Sanusi Dantata da ke unguwar koki da kotun ta ambata a baya.
 Kotun ta dage zamanta zuwa ranar 19 ga Afrilu, 2023 don ci gaba da ambato.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...