Akwai yiwuwar bashin da a ke bin Nijeriya ya kai Tiriliyon 45 a shekarar 2022, in ji DMO

Date:

 

Ofishin Kula da Basussuka, DMO, ya ce akwai yiyuwar yawan basussukan da a ke bin Nijeriya ya kai Naira tiriliyan 45 a shekarar 2022 da mu ke ciki.

Wannan bayanin ya zo ne a yayin da gwamnati ke shirin ƙara ciyo bashin Naira tiriliyan 6.39 domin cike giɓin kasafin kuɗin shekarar 2022.

Patience Oniha, Darakta-Janar ta DMO ce ta bayyana hakan a wata hira da ta yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, a yau ranar Alhamis a Legas, yayin da take magana a kan wani shiri na wayar da kan jama’a da ofishinta ya shirya.

Oniha ta bayyana cewa gibin kasafin kudin na shekarar 2022 ya kai Naira tiriliyan 6.30, wanda yai daidai da kashi 3.46 na GDP na kasar.

Ta ce, sai an ciyo bashi a gida da waje da kuma kuɗaɗen da a ka samu wajen jimginar da kadaroein gwamnati sannan za a iya cike giɓin kasafin kudin.

“Kimanin Naira Tiriliyan 2.57 za su fito daga gida, Naira Tiriliyan 2.57 daga kasashen waje, Naira Tiriliyan 1.16 daga raguwar lamuni da aka samu tsakanin bangarorin biyu da kuma Naira Biliyan 90.7 daga kudaden da ake samu daga hannun jari,” inji ta.

Sai dai kuma ta ce ciyo bashin kuɗaɗe domin cike giɓin kasafin kudi da samar da gine-gine da ababen more rayuwa ba abu bane maras kyau.

Oniha ta ƙara da cewa gwamnatocin ƙasashen duniya na ranto kuɗaɗe domin yin Aiyukan ci gaba a kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...