ZARGIN DUKAN MATAR AURE YAR SHEKARU 55 A DUNIYA YA SANYA KOTU TA AIKE DA WANI MATASHI GIDAN DAN KANDE.

Date:

Daga Ibrahim Aminu Riminkebe

Babbar kotun shari’ar mai lamba 1 dake zaman a kofar kudu karkashin jagorancin mai Malam Ibrahim Sarki Yola, ta aike da wani matashi mai suna Ghazali Abdullahi Goron Dutse wanda aka fi sani da Ghaza bisa zargin sa da  dukan wata matar aure mai suna Halima Abdulhamid yar kimanin shekaru 55 a duniya.

Kadaura24 ta rawaito tun da fari dai alamarin ya samu asali ne biyo wata hatsaniya data shiga tsakanin su a unguwar Kuntau dake yankin karamar hukumar Gwale ta jihar kano, a lokacin dashi Ghazali Abdullahi Goron Dutse yazo da wata sabuwar mota unguwar ta Kuntau domin ya nuna yan uwan sa motar, wanda a nan Ghaza yayi ta faman danna karar motar babu gaira babu dalili kana a lokacin da Malama Halima Abdulhamid tayi masa magana shi bata yi masa dadi ba.

Wanda kuwa fiowar sa daga cikin motar ke da wuya ya fara gayawa Halima Abdulhamid bakan maganganu har takai yayi mata duk a sassan jikin nata baya ga samun raunika, abunda ya sanya Uwar gida Halima Abdulhamid ta garzaya zuwa ga jami’in tsaro domin neman hakkin nata.

Sai Kuma bayan da sanda mai gabatar da Kara wato Sepito Suleman ya gama karanta masa kunshin tuhume tuhuman da ake yi masa, daga bisani mai Shari’a Ustaz Ibrahim Sarki Yola ya juya ga Ghazali Abdullahi Goron Dutse ya ya musanta wasu daga cikin bayanan da Ita Halima Abdulhamid ta yiwa kotun amma Kuma ya tabbatarwa da kotun cewar ya fadawa Ita Uwar gida Halima Abdulhamid mutuniyar banza ce ya Kuma dake ta.

Kana Kuma bayan jin ko wane bangare ne Alkalin kotun mai Shari’a Ustaz Ibrahim Sarki Yola yayi umarni ga jami’an gidan gyran hali da tarbiya dasu yi awon gaba dashi har zuwa ranar 16 ga watan jibi domin dorawa daga ina aka tsaya.

Cikin halin zuba da kwalla uwar gida Halima Abdulhamid ta bayyana namema labarai cewar ko shakka Ghazali Abdullahi Goron Dutse ya ci zafin ta a bayyanar jama’a, ta Kuma nuna farin cikin yadda kotun ta fara nema mata hakkin ta, ta Kuma yi Kira ga mahukuntan dasu shigo cikin wannan alamarin domin ganin an kwatar mata hakkin nata na cin zafi ta hanyar duka da ake zargin yayi mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...

Na riga Kwankwaso shiga harkokin Siyasa – Sanata Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jaridun Amurka sun bankado Tsare-tsare uku da sojojin Amurka ke yi don tunkarar Najeriya

Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar...

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...