Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, ya ƙaddamar da takarar neman shugabancin ƙasar a babban zaɓe na 2023 mai zuwa a jam’iyyar adawa ta PDP.
Atiku, wanda ya shafe shekara fiye da 15 da suka wuce yana neman shugabancin Najeriya, ya ce zai mayar da hankali kan ɓangare uku idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.
Da ya ke jawabi yayin taron, Atiku ya ce gwamnatinsa za ta zama gada tsakanin mulkin dattijai da na matasa.
“Gwamnatinmu za ta zama kamar gada ce [da za ta haɗa] tsakanin mulkin dattijai da na matasa.”
Ya ci gaba da cewa: “A ƙarƙashin mulkina, zan mayar da hankali kan ɓangare biyar masu muhimmanci; haɗin kan Najeriya, tsaro, tattalin arziki, ilimi, ciyar da ɓangarorin gwamnatin tarayya gaba da ƙara musu iko.”
Bikin ya gudana a International Conference Centre da ke Abuja a yau Laraba.