Daga Abdullahi Alhassan Kaduna.
Dakta Maji Peterx shine Babban Daraktan a Kungiyar mai yunkurin wazan da zaman lafiya,a tsakanin Al’ummomin daban daban a Najeriya, mai Suna Equil Access lntetnational (E A I),dake aikin tabbatar da kare al’ummar Najeriya ,da ma samar da fahimtar juna, musamman ma,a jahohin a kasan nan, da suka hada da Benue Filato Kaduna da Kano.
Dakta Peterx yace “fatan mu shine ganin an kare afkuwar tashin hankalin, ana samu fahimtar juna tsakanin Al’ummomin daban -daban dake rayuwa a Najeriya, wan nan yasa muka kira wan nan taro da ya hada da Shugabannin Kungiyoyin Matasa, Jami’an tsaro, Sarakuna, Shugabannin Addinai, da suka hada da J,N,I C.A.N, da Mata dama Masu bakata ta musamman,ko “People with disabilities a Turance,don ganin an tattauna hanyoyin da za’a bi na dakile tashin hankalin a yankunan su.
Babban Daraktan,ya kara da cewar manufar wannan taron shi ne saka Jami’an tsaro, Shugabanin Al’umma, Mata da Matasa, dake Kaduna don ganin an cimma hanyoyin Kare al’ummar Najeriya, shine ma taken taron, Samar da zaman lafiya a yankunan dake fama da matsalar tsaro da rikece-rikice, don kawo karshen ta a yankunan da suka fito dama Najeriya baki daya.
Dakta Maji ,yana wannan jawabin ne a taron da suka kira a Kaduna tare haɗin gwiwa da takwarar ta Gidauniyar wanzar da zaman lafiya ta CLEEN Foundation,Mai taken “Kare Al’ummar Najeriya”
“Wannan taron zai bude Kofar fahimtar juna tsakanin Al’ummomin, ta hanyar da kowa zai zama mai hannu da shuni ko mai ruwa da tsaki kan harkar tsaro muna fatan abinda aka tattauna a nan kowani Mutum wakilin Al’ummar su ne ,kuma zai gida ya fadakar da su kan wan nan aiki da suka sa a gaba na kare afkuwar tashin hankali a kasar nan.
Shi kuwa Jami’in Shirye Shirye na Gidauniyar ta CLEEN Foundation,Mista Ebere Mbeagbu,yace yayi wani nan taron zai fadakar da Jami’an tsaro,da Shugabannin Al’ummomin kan yarda zasu kare afkuwar tashin hankali a cikin yankunan su,tare kuma da hanyoyin dakile faruwa ma shi tashin hankalin,haka kuma bai basu dama ta hanyar da za subi na ganin cewa sun bada gudunmawa cikin harkokin samar da zaman lafiya.
Mista Ebere Mbeagbu, ya kara da cewar irin wan nan zai magance rashin fahimta tsakanin jami’an tsaro da Mutanen gari, haka kuma zai sa cewar Mutanen suji cewar suna da rawa da zasu taka kan samar da tsaro kasancewar shi tsaro abune dake da bukatar sa hannun kowa.
“Muna fatan cewar a karshen watan taron ya zama cewar mahalarta taron sun koyi abubuwan da zasu habbbaka aiyukan da muka sa gaba na Kare Al’ummar Najeriya, haka kuma farfaɗo da zaman lafiya a tsakanin Al’ummomin daban daban da ke rayuwa a Najeriya.
A nashi Jawabin yayin wan nan taron Mista Samuel Aruwan,wanda shine Kwamishinan Tsaro da harkokin cikin gida na jahar Kaduna,kira yayi da Al’umma da su rika kai rahoton duk wani abu da basu amincewa ba ga jami’an tsaro don ɗaukar matakan kariya daga jami’an tsaron,
Inda ya kara da cewar Gwamnati a shirye take na ganin ta kare rayuka da kuma dokiyuyin Al’umma don haka akwai bukatar sanar da jami’an tsaro duk halin da aka ganin na tashin tashina ne don kawo musu daukin gaggawa.
Mista Aruwan yace “nuna cikin wani mawuyacin hali na matsalar tsaro saboda haka, jami’an tsaron mu baza su lya karade duk ko wani sakuna da lunguna na fadin wan nan jahar ba,saboda haka dole ne Al’umma ltama ta bada gudunmawa ta hanyar bawa jami’an tsaro bayanai da zamu taimaka musu akan aikin su.
Ya kuma ce zamu lya magance rashin hankali da kuma kalubalen tsaro ldan muka hada hannu wajen yin aiki tare, ta hanyar sanar da jami’an tsaro, Gwamnatin jahar Kaduna a shirye take na ganin ta karbi duk wani abu da zai kawo mana zaman lafiya a Jahar mu.
Su kuwa mahalarta wan nan taron cewa sukayi taron yazo kan lokacin da ya kamata,kuma zai kawo karshen rikici da wanzuwar zaman lafiya da ma fahimtar juna a jahar.
Imam Shafiu Hassan,wani Malamin addini ne, daga karamar hukumar Kajuru, ya ce yayi shi yanzu jakadan zaman lafiya ne, haka kuma sun rungume zaman lafiya a yankunan su.
Shima Mista Titus Dauda wanda shine Dagacin kufana a karamar hukumar Kajuru,yace yayi wan nan taron bitar ya basu damar sanin hanyoyin da zasu bi na magance rikicin a yankin su,ta hanyar hada kai da jami’an tsaro,na ganin cewa sun kare rayuka da ma duniyoyin al’ummar su.

