Daga Sayyadi Abubakar Sadeeq
Rundunar ‘yan sanda a Kano na shirin cafke wani shahararren mai sharhi kuma mai sharhi kan al’amuran siyasa, Bashir Gentile, kan sukar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, a wasu shirye-shiryen rediyo na cikin gida, kamar yadda Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito.
Bashir Gentile, wanda na hannun dama ne ga tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau, kuma mai taimaka wa shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan a halin yanzu.
A baya-bayan nan dai da dama daga cikin masu sukar gwamnan suna fuskantar tuhuma a gaban Alkalai bayan ‘yan sanda sun kama su.
Rahotanni sun nuna cewa bayan yunkurin kama Bashir Gentile ya ci tura, a yanzu ‘yan sanda sun gayyace shi domin ya amsa tambayoyi kan karar da aka shigar a kansa.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Kiyawa, ya ce bai da masaniya akan gayyata ko shirin kama Bashir Gentilen.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce zai kara yin bincike kan lamarin.