Daga Sayyadi Abubakar Sadeeq
Tsohon Kwamishinan ƙasa da safayo a gwamnatin tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kuma na ƙusa a tafiyar Kwankwasiyya a Kano, Hon Yusuf Bello Ɗambatta, ya ce sakamakon ƙin amincewa da shawarar su ta yadda za’a kawo wa tsarin Kwankwasiyya nasara ta sanya suka yanke shawarar ci gaba da zama a jam’iyyar PDP.
A wata tattaunawa da akayi dashi a kafar talabijin ta Tambari, Ɗambatta ya zargi masu yi musu kallo sun ci amanar tsarin Kwankwasiyya a matsayin rashin adalci tsantsa.
Sannan ya kafa misalai da irin raba gari da wasu daga cikin ƙusoshi a tafiyar siyasar tsohon Gwamna Dr Rabiu Musa Kwankwaso da rashin tuntuɓa da barin yara suna cin zarafin shugabannin tafiyar ba tare da an ɗauki mataki ba.
Da Mai an dade ana ta rade-raden cewa irin su Yusuf Danbattan da Wasu jiga-jigai a tafiyar Kwankwasiyya su na nunawa juna yatsa Sakamakon abun da Suka Kira da Rashin girmamawar da Wani tsagi na tafiyar basa yiwa wani tsagin.
Tun dai a makon daya gabata ne Kadaura24 ta rawaito Su Yusuf Bello Danbatta da Dr adamu Yunusa Dangwani da Zainab Audu bako da Hon. Dan buran Abubakar Nuhu Sun kai ziyarci ga Sanata Ibrahim Shekarau Wanda ake Ganin Kamar sun je wajen sa be domin suyi bikonsa ya dawo jam’iyyar PDP.