Daga Sayyadi Abubakar Gwagwarwa
Kungiyar Kafofin yada labarai ta Arewa sun neman Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin gaggawa don tallafa musu don ci gaba da gudanar da aikin su Saboda da yayi tashin gwauron zabi inda ake sayar da shi N720 zuwa N730 kowace lita.
Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan Shugaban l Gidan Talabijin na Liberty TV da Liberty Radio, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Amintattun Kungiyar shi ne ya yi wannan roko a Abuja ranar Talata, yayin da farashin man fetur da dangoginsa suka yi tashin gwauron zabo, Kuma ake fuskanta karancin wutar lantarki a fadin kasar nan.
“Abu ne mai wahala a ci gaba da watsa shirye-shirye a wannan lokaci, saboda man dizal ya haura N720-N750 kowace lita,” in ji Ramalan.
“Yana da matukar wahala kafafan yada labaran mu su cigaba da aiki kuma ban san yadda za mu shawo kan matsalar ba saboda kashi 100 cikin 100 na gidajen Talabijin da Rediyon mu suna aiki da dizal kuma babu hasken wutar lantarki.”
Ramalan yace yana da matukar wuya mu iya cigaba da wannan Kasuwanci kasuwancin kuma idan ba a yi wani abu ba don dawo da wutar lantarki da kuma rage farashin Diesel, bamu da zabin da ya wuce mu rage yawan shirye-shiryen da muke Kuma mu rage Ma’aikata Saboda baza mu iya cigaba da gudanar da Kafafen yada labaran a haka ba.