Mai Mala zai dawo kan kujerarsa ta shugabancin riƙon APC

Date:

 

Ga dukkan alamu, Shugaban Kwamitin Riƙo na Jam’iya mai mulki APC kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne zai jagoranci babban taron APC na ƙasa a ranar 26 ga watan Maris.

Jaridar Punch ta jiyo cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci Buni ɗin da ya jagoranci taron, amma ya masa zazzafan kashedin cewa ba za a ƙara ɗage ranar yin Babban taron jam’iyar na ƙasa ba.

Majiyoyi sun shaida wa Punch cewa Buhari ya ɗauki wannan matakin ne bayan ganawa da ya yi da wasu jiga-jigan jam’iyar a Landan.

Da ga cikin waɗanda su ka baiwa Buhari shawarar ɗaukar wannan matakin akwai Antoni-Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, wanda ya nuna wa shugaban ƙasar illar da za a iya samu ta ɓangaren Shari’a.

Haka-zalika an jiyo cewa, bayan da a yanzu shugaban ƙasar ya nuna ba shi da wani ɗan takara a zaben shugaban jam’iyar na din-din-din, yanzu gurbin ya zamto a bude, inda kowa zai iya nema.

Hakan kuma, in ji majiyoyi, ya nuna rashin tabbas a kan rabon muƙamai na shiyya-shiyya da jam’iyar ta fitar a makon da ya gabata.

Haka kuma a ganawar ta birnin Landan, Buhari ya musanta bada umarnin cire Buni da kuma maye gurbinsa da Gwamna Abubakar Sani Bello kamar yadda Gwamna Nasir El-Rufai ya faɗa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...