Daga Sayyadi Abubakar Sadeeq
Kotun majistare mai lamba 58 a jihar Kano karkashin jagorancin Aminu Gabari ta soke belin da tun farko ta bayar ga mai sukar Gwamnatin kano a kafafen sadarwar zamani , Mu’a’zu Magaji Dansarauniya kan rashin halartar kotun har sau 3 domin amsa tuhumar da ake masa na bata sunan gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Haka zalika kotun ta bayar da umarnin kama shi tare da mika sammaci ga mutane biyun da su tsaya Masa da su bayyana a kotun ranar 28 ga Maris na Wannan Shekara.
Karin bayani na nan tafe…