Daga Isa Ahmad Getso
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Gidan Rediyon Tarayyar Kaduna FRCN, wanda aka fi sani da Rediyon Najeriya Kaduna murnar cika shekaru 60 da kafuwa.
Kadaura24 ta rawaito a cikin sakon taya murna da kakakinsa, Femi Adesina, ya fitar a ranar Litinin a Abuja, Buhari ya yaba wa gidan rediyon kan rawar da ta taka wajen hada kan al’ummar Najeriya.
An nadi sakon bidiyon ne da harshen Hausa domin tunawa da wannan kafa ta Radiyon Tarayya na kaduna.
Shugaban ya kuma yabawa gidan rediyon bisa kokarin da ya yi na maido da zaman lafiya bayan kammala ayakin basasa a Nigeria.
Buhari ya yaba wa gidan rediyon kan shirye-shiryensa masu ilmantarwa, fadakarwa da kuma nishadantarwa wadanda suka kara kayatar da masu sauraronta a fadin Najeriya da makwaftan kasashe.
Ya bukaci mahukuntan gidan rediyon Najeriya Kaduna da su ci gaba da abun da akan san gidan rediyon na hada kan al’umma da wayar da kan al’umma kan muhimman batutuwan da za su inganta ci gaban kasa.”