Daga Sajida Ahmad Takai
Manya a tafiyar tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wadanda alamu suka nuna cewa ba zasu bar jam’iyyar PDP ba ko da kuwa Kwankwaso ya barta sun Ziyarci Tsohon abokin burmin uban gidan su a Siyasa Malam Ibrahim Shekarau Sanatan kano ta tsakiya.
Rahotannin sun bayyana cewa Waɗanda suka ziyarci malam Shekarau jagoran G7 sun hadar da Yusuf Bello Danbatta, Abubakar Nuhu Danburam da Zainab Audu Bako.
Rahotanni sun bayyana cewa, sun ziyarci Sanata Shekarau yau a gidansa dake babban birnin tarayya Abuja, domin zawarcinsa zuwa jam’iyyar PDP.
Sai dai har yanzu babu cikakken bayanin makasudin ganawar tasu m, Amma dai ana Ganin bazata rasa nasa da yadda yanayin Siyasa a kano ke ta juyawa ba.
Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito Cewa akwai Wasu cikin jiga-jigan tafiyar Kwankwasiyya da suka ce su baza su bishi Sabuwar jam’iyyar NNPP da Kwankwason yake Shirin shiga Zuwa Karshen watan nan kamar yadda ya fada.